A ci gaba da ayyukanta na ceto wadanda lamarin Garkuwa da mutane ya rutsa da su a yanzu haka a wasu sansanonin ‘yan bindiga da ke jihar.
A ranar 25 ga watan Fabrairu, 2022, rundunar ‘yan sandan hadin gwiwa tare da sojoji da aka tura tare Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara sun yi nasarar ceto mutane bakwai (7) da aka yi garkuwa da su ‘yan asalin kauyen Chibade a karamar hukumar Rijau ta jihar Neja.
Wadanda abin ya shafa a yayin zantawar da su, sun sanar da ‘yan sanda cewa, a ranar 21 ga watan Fabrairu, 2022 ‘yan bindiga da dama sun dira a kauyensu (Chibade) inda suka yi awon gaba da bakwai daga cikinsu zuwa inda ba a san inda suke ba a dajin Dansadau na jihar Zamfara.
Jami’an hadin gwiwa na ‘yan sanda da na soji a yayin da suke gudanar da wani katafaren aiki a wani daji da ke kewayen Dansadau, sun yi nasarar ceto wadanda abin ya shafa tare da kai su asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau inda aka duba lafiyarsu.
A cewar Mai magana da yawun Rundunar SP Muhammed Shehu, Za a mika dukkan wadanda abin ya shafa ga kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja domin daukar matakin da ya dace.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, CP Ayuba N. Elkana psc(+) ya taya wadanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu murnar samun ‘yancinsu tare da tabbatar wa da jama’ar ‘yan sandan ci gaba da jajircewa wajen kawar da duk wani nau’i na miyagun ayyuka a jihar.