Kwamishinan yan Sandan jihar Zamfara, CP Ayuba N. Elkanah psc+ ya ziyarci gidan gyaran Hali da ajiya na Gusau, domin tabbatar da kawar da duk wata barzana da zata iya Kawo cikas ga kokarin da rundunar su ke yi Wajen yaki da matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Kazalika ziyarar tasa wani bangare ne, na irin kokarin da rundunar su ke yi, domin tabbatar da gidajen gyaran Hali a jihar Baki daya na cikin yanayi na kwanciyar hankali, da kuma kare su daga Bata gari.
Mai magana da yawun Rundunar SP Muhammad Shehu ne ya sanar da hakan, cikin wata sanarwa da ya aikowa da Jaridar Dimokuradiyya a daren Jiya Litinin, inda yace kwamishinan ya kasance tare da rakiyar wasu manyan jami’an rundunar, tare da Yi musu alkawarin cewa kullum kofar su a bude take domin karbar duk wani roko da ya shafi tsaron gidajen gyaran Halin.
Da yake godiya bisa ziyarar da akai Kai musu, babban kwanturolan hukumar Lura da gidajen gyaran Halin, ya kuma godewa rundunar Yan Sandan jihar Zamfara, duba da yake suke Basu taimakon da ya Kamata a Koda yaushe.
Ya kuma yiwa kwamishinan alkwarin cewa ofishinsa zai Yi aiki kafada da kafada da rundunar wajen basu rahotan duk wani abu da zai Zama barazana ga tsaron gidajen gyaran Halin.