IMG-20190904-WA0002

RUSA MASALLACI: An Yi Tir Da Wike, An Yaba Ganduje

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama da taimakon talakawa da sauran jama’a marasa karfi ta Rigar ‘Yanci wato “Rigar ‘Yanci International Foundation For Less Privilege” ta yi tir gami da Allah wadai da rusa babban Masallacin Juma’a na garin Fatakwal da Gwamnan Ribas Wike yayi, inda ta bayyana matakin rusa Masallacin a matsayin abin takaici.

Da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta kira a Kaduna, babban Daraktan Ƙungiyar Injiniya Usman Musa yace, ta’adin da Gwamnan na Ribas ya yi abin damuwa ne wanda ya karya dokar kasa, domin ayyana wata jiha a matsayin ta wani addini ya saba doka, kuma tabbas Ƙungiyar za ta dauki matakin da ya dace akan gwamnan sakamakon wannan katobara da ya yi wacce zata iya wargaza zaman lafiyar ‘yan Najeriya baki daya.

Injiniya Usman Musa ya kara da cewar suna sane da kokarin karyata labarin rusa Masallacin da Gwamnan ya yi, amma wannan maganar shirme ce domin masallacin a fili ya ke kowa ya sani, kuma mun tuntubi sakataren masallacin Ustas Aliyu Sadiq wanda ya tabbatar da rusa katafaren masallacin a ranar 20 ga watan Agustan wannan shekara ta 2019.
Kungiyar ta Rigar ‘yanci ta kuma bukaci jama’ar musulmi na jihar Ribas da su cigaba da zama lafiya da martaba doka, kuma da yardar Allah Gwamna Wike zai ga sakamakon aikin shi, da ikirarin da yayi na cewar Jihar Ribas ta Kiristoci zalla ce.

Kungiyar rajin Kare hakkin Bil’adam da taimakon talakawan ta kuma yaba gami da yin jinjina ga mai girma Gwamnan jihar Kano Ganduje, bisa matakin da ya dauka na maka Gwamna Wike Kotu akan rusa Masallacin, da yadda Gwamnan na Kano ya bada dama ga kiristocin da ke zaune a jihar Kano su zauna cikin lumana da kwanciyar hankali ba tare da tsangwama ba, kasancewar jihar Kano ta fi kowace jiha a Arewa yawan kiristoci da ke zaune ciki, amma Ganduje bai taba barazana ga kowa ba, lallai ya dace sauran Gwamnonin Najeriya su yi koyi da Ganduje.

Dangane da kisan ‘yan Najeriya da yanzu haka yake faruwa a kasar Afirka ta Kudu kuwa, Ƙungiyar ta Rigar ‘yanci ta bukaci ‘yan Najeriya da su zauna lafiya kada su dauki doka a hannun su, su jira su ga abin da gwamnati za ta yi akai, sannan sun ankarar da jama’ar Afirka ta Kudu cewar ‘yan Najeriya ba su bane matsalar su, saboda haka kisa da kone dukiyoyin su ba zai warware musu matsalar da suke ciki ba.
Sannan daga karshe sun yi kira ga ‘yan Najeriya baki daya da su cigaba da zama lafiya da juna ba tare da nuna wariya ko tsangwama a tsakanin su ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *