• About Us
  • Blog
  • Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana gabda fara ginin masana’antun Iskar Gas a Jihar
  • Home
Monday, June 5, 2023
  • Login
Dimokuradiyya
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio
No Result
View All Result
Dimokuradiyya
No Result
View All Result
Home Labarai

RUSAU: ‘Yan Kasuwa Sun Dukufa Yi Wa El-Rufai Addu’a

Mustapha Haruna Dabai by Mustapha Haruna Dabai
September 18, 2019
in Labarai
Reading Time: 2 mins read
0 0
0
1
SHARES
6
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

‘Yan kasuwa a jihar Kaduna sun fara gudanar da addu’o’i na musamman a kan gwamnatin jihar Kaduna sakamakon manufar gwamnan jihar na rusa wasu manyan kasuwannin jihar tare da sake gina su a tsarin ginin zamani.

Rahoton jaridar Daily Trust ta labarto ‘yan kasuwan na bayyana rashin gamsuwarsu da manufar gwamnatin na zamanantar da kasuwanni, musamman duba da cewa ba ta ba su wani wurin da za su ci gaba da gudanar da kasuwancinsu ba.

A cikin wata hira da aka yi da gwamnan jihar Kaduna, ya tabbatar da burinsa na fadada wasu kasuwannin jihar tare da zamanantar da su, da suka hada da Kasuwar barci, kasuwar Sabon gari da kuma babbar kasuwar Kaduna na Sheikh Gumi.

Gwamnan ya ce; “Kasuwannin nan suna bukatar a fadada su, kuma zamu fadada su, kuma zamu gina sabbin kasuwanni na zamani a unguwanni inda mutane za su iya kama hayan shaguna, daga nan zamu wuce Zariya da Kafanchan don gina sabbin kasuwanni, dole ne kawai mu gyara Kaduna.” Inji shi. Haka zalika Gwamnan ya kara da cewa za su gina sabbin kasuwanni a garin Rigasa na karamar hukumar Igabi, da kuma garin Zonkwa.

Sai dai wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun bayyana damuwarsu game da wannan aiki, musamman ‘yan kasuwan barci, wanda suka ce sun fara addu’ar ka da Allah ya bai wa gwamnan ikon aiwatar da wannan manufa.

Wani Tela dake kasuwar barci, Sani Muhammad ya bayyana cewa: “Mun fara addu’o’i na musamman a kan wannan manufa, saboda yawancinmu muna cikin damuwa game da aikin, saboda zamu rasa abin yi idan aka fara aikin.”

Shi ma wani mai suna Jafaru Madobi ya ce: “Wannan zalunci ne, saboda a yanzu haka duk mun dimauce, mun sani idan aka rusa kasuwan ba zamu sake samun shago ba, mu jari muke so daga wajen Gwamnan ba aikin fadada kasuwa ba.”

Haka zalika wani dan gwanjo mai suna Usman Mani ya ce: “Mun shiga damuwa tun bayan maganar da gwamnan ya yi saboda bamu da na yi, me yake su mu yi, tun da yawancin bamu da kudin da zamu iya kama shago? Kuma bamu ji ya yi maganan biyan kudin fansan shagunan da zai rusa ba.”

Previous Post

Babban Limamin Agaie A Neja Ya Rasu Yana Da Shekaru 91

Next Post

JARABAWAR NECO: Gwamnatin Neja Ta Biya Wa Dalibai Bashin Miliyan 200

Next Post

JARABAWAR NECO: Gwamnatin Neja Ta Biya Wa Dalibai Bashin Miliyan 200

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result
  • Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    Ya ce mun shi Dillalin Motoci ne, bayan mun yi aure na gane Makanike ne

    2601 shares
    Share 1040 Tweet 650
  • Batun Dakatar Da Opay Da Palmpay, CBN Ya Bayyana Gaskiyar Zance

    2342 shares
    Share 937 Tweet 586
  • Da Ɗumi-Ɗuminsa: Ƙazamin Rikici Ya Kaure Tsakanin Shugaban Ƙungiyar CAN Da Isa Ashiru Kudan

    2131 shares
    Share 852 Tweet 533
  • Sai na yi lalata da kai na kwanaki 4 babu ƙaƙƙautawa sannan zan taimaka maka, Wata mata ga saurayi

    1907 shares
    Share 763 Tweet 477
  • Ga Irinta Nan: Budurwa Ta Koka Bayan Saurayinta Ya Ƙi Amsar Cikin Da Ya Ɗirka Mata

    1440 shares
    Share 576 Tweet 360
Manyan Jami’an ‘Yan Sanda 130 Ke Fuskantar Bincike Kan Rashin Da’a

‘Yan Sanda Sun Ceto Wasu Yara Tara Da Aka Sace A Zamfara

June 5, 2023
NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5  Cikin Shekaru Hudu – Rahoto

NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5 Cikin Shekaru Hudu – Rahoto

June 5, 2023
Da Dumi-Dumi: Anyanka Ta Tashi:Kungiyar NLC Za Ta Tsunduma Yajin Aikin Gama Gari

Cire Tallafi: NLC Ta Yi Watsi da Taron FG, Ma’aikatan Wutar Lantarki Zasu Shiga Yajin Aiki

June 5, 2023
Gwamnatin Kano Ta Kori Jami’an Dake Kula Da Cibiyoyi Hajji, Ta Rusa Otal

Gwamnatin Kano Ta Kori Jami’an Dake Kula Da Cibiyoyi Hajji, Ta Rusa Otal

June 5, 2023
Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Zulum da Buni Sun Halarci Jana’izar Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno

Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Zulum da Buni Sun Halarci Jana’izar Tsohon Sakataren Gwamnatin Borno

June 5, 2023
Janye Tallafin Fetur: FG Da TUC Sun Shiga Ganawa A Abuja

Janye Tallafin Fetur: FG Da TUC Sun Shiga Ganawa A Abuja

June 4, 2023
Manyan Jami’an ‘Yan Sanda 130 Ke Fuskantar Bincike Kan Rashin Da’a
Labarai

‘Yan Sanda Sun Ceto Wasu Yara Tara Da Aka Sace A Zamfara

June 5, 2023
NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5  Cikin Shekaru Hudu – Rahoto
Labarai

NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5 Cikin Shekaru Hudu – Rahoto

June 5, 2023
Da Dumi-Dumi: Anyanka Ta Tashi:Kungiyar NLC Za Ta Tsunduma Yajin Aikin Gama Gari
Labarai

Cire Tallafi: NLC Ta Yi Watsi da Taron FG, Ma’aikatan Wutar Lantarki Zasu Shiga Yajin Aiki

June 5, 2023
Manyan Jami’an ‘Yan Sanda 130 Ke Fuskantar Bincike Kan Rashin Da’a

‘Yan Sanda Sun Ceto Wasu Yara Tara Da Aka Sace A Zamfara

June 5, 2023
NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5  Cikin Shekaru Hudu – Rahoto

NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5 Cikin Shekaru Hudu – Rahoto

June 5, 2023
Da Dumi-Dumi: Anyanka Ta Tashi:Kungiyar NLC Za Ta Tsunduma Yajin Aikin Gama Gari

Cire Tallafi: NLC Ta Yi Watsi da Taron FG, Ma’aikatan Wutar Lantarki Zasu Shiga Yajin Aiki

June 5, 2023

Twitter

Archives

Recent Posts

  • ‘Yan Sanda Sun Ceto Wasu Yara Tara Da Aka Sace A Zamfara
  • NIS Ta Samar Da Fasfo Miliyan 4.5 Cikin Shekaru Hudu – Rahoto
  • Cire Tallafi: NLC Ta Yi Watsi da Taron FG, Ma’aikatan Wutar Lantarki Zasu Shiga Yajin Aiki

Quick Links

  • Tsaro
  • Siyasa
  • Labarai
  • Wasanni
  • Kasuwanci
  • Rikicin Duniya

Contact Us

info@dimokuradiyya.com.ng

0809 912 4425 +234 809 912 4425

No. 218 Mogadishu layout Kaduna City Center Ahmadu Bello way kaduna. Kaduna, Nigeria 800273

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

No Result
View All Result
  • Home
  • Labarai
  • Siyasa
  • Rahotanni
  • Wasanni
  • Rikicin Duniya
  • Nishadi
  • More
    • Kasashen Ketare
    • Kiwon Lafiya
    • Ilimi
    • Kasuwanci
    • Noma Da Kiwo
    • Labarun Mako
    • Talla
    • Masarautu
    • Babu Maraya
    • Addini
      • Wa’azin Kirista
    • Girke-Girke
    • Waiwaye
    • Marubutanmu
    • Wasiku
    • Ni’ima Dai Mata
    • Tsaro
    • Bidiyo
    • Audio

Copyright © 2023 Dimokuradiyya Media Services LTD.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In