Wata katanga da ta rushe a wata makaranta da ke Legas, Covenant Point Academy da ke Ajose Street, a unguwar Amukoko a jihar Legas, ya yi sanadin mutuwar yara biyu, Samat Saheed da wata yarinya da har yanzu ba a tantance ba.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa yarinyar mai shekaru tara ta wuce gaban makarantar domin tafiya inda ta nufa a unguwar yayin da Samat mai shekaru uku ke wasa a katangar makarantar, kusa da shagon mahaifiyarsa lokacin da katangar ta rushe.
Wakilinmu ya tattaro cewa, a lokacin da katangar ta danne kananan yaran, ta murkushe kan Samat, inda nan take ya mutu, yayin da yarinyar ‘yar shekara tara ta rasa hayyacinta, kuma rahotanni sun ce ta mutu jim kadan da faruwar lamarin.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wani ganau, Ganiyu Ayeloja, ya ce mazauna garin da lamarin ya faru sun sanar da yan sanda, inda ya jara da cewa an kama mai makarantar.
Karanta kuma: Gwamnatin Legas Ta Bada Umarnin Komawa Makarantu
Ya ce, “’Yan sanda sun zo, suka kama mai ginin makarantar. Ginin ba shi da ginshiƙai, kawai sun tara tubalai ne. Ba a tsara ginin ba kwata-kwata; babu waya, babu ginshiƙi, kuma babu abin da zai riƙe ginin shi ya sa ya faɗi cikin sauƙi.
“Abin takaici ne cewa yaran biyu suna kusa da wannan yanki lokacin da ta rushe. Daya daga cikin iyayen yaran yana da wani shago kusa da ginin makarantar, dalilin da ya sa yake wurin kuma nan da nan aka sanar da iyayensa.
“A jiya ne aka kira Oba na Ijora land a kan lamarin kuma kowa yana tausayawa iyalan wadanda suka rasu. Jama’a daga hukumar kula da gine-gine ta jihar Legas sun zo duba ginin da safiyar ranar Lahadin nan.”
Wani mazaunin unguwar mai suna Akinniyi Akinwale ya bayyana cewa yarinyar ‘yar shekara tara tana gudanar tafiya ne a lokacin da wannan mummunan lamari ya same ta.
Ya ce, “Katangar da ke gaban makarantar ta fado a kan su biyun. Yarinyar da ta rasu an tura ta ne zuwa wannan titi, don haka babu wanda ya san iyayenta a can amma an kai ta asibiti bayan faruwar lamarin kuma sai da dare ne iyayenta suka fara nemanta aka sanar da su mutuwarta.”
Da yake mayar da martani kan lamarin, wani tsohon shugaban Cibiyar Gine-gine ta Najeriya, Kunle Awobodu, ya ce tubalan da ake gina gine-ginen a zamanin nan sun yi rauni sosai, kuma ba su da inganci, inda ya bukaci injiniyoyin da ke gina gine-gine da sauran su da su daina amfani da kayayyakin da ba su da inganci.
Ya ce, “Wannan abin takaici ne. Mu da ke cikin masana’antar gine-gine sun ba da fifiko kan barazanar karfi na yanayi ko matsin lamba a kan gine-gine, don jure irin wannan matsin lamba musamman a yankin da ke da iska mai karfi, akwai bukatar gabatar da ginshiƙai.
“Yawancin tubalan da ake gina gine-gine a zamaninmu suna da rauni sosai kuma ba su da inganci; yawanci inci shida ne da kauri mil 150 wanda ba ya iya jure karfin iska wanda hakan ya sa ya zama wajibi mu kara taka tsantsan,” inji shi.
A wani labarin kuma: Tsawaita Yajin Aiki: FG Za Ta Gana Da ASUU A Kotun Masana’antu Ranar Litinin
Gwamnatin tarayya ta ce za ta gana da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a kotun masana’antu ta kasa (NICN) a ranar Litinin domin yanke hukunci kan tsawaita yajin aikin.
Dakta Chris Ngige, Ministan Kwadago da tabbatar da nagartar aiki ne ya bayyana haka ranar Lahadin nan a Abuja a wata wasika da ya aikewa magatakardar NCN, mai kwanan watan 8 ga watan Satumba.