Mamakon ruwan sama dauke da iska ya yi sanadiyar salwantar rayukan Mutane 19 yayin karin wasu 50 kuma suka yi batan dabo a kasar Jamus.
Har wa yau wannan Ibtila’i yayi sanadiyar shafe gidaje da dama a sanyin safiyar Alhamis din nan.
Wannan lamari da ba a saba ganin irinsa ba, ya kuma shafi makotar kasar ta Jamus kamar su Luxemburg da Holand da kuma Belgium, inda nan kuma mutane 2 suka rasa ransu.
Jihohin Rhineland ta arewa da kuma Rhine-Westphakia na daga cikin Jihohin da lamarin ya fi ɓarna inda ya yi sanadin aman teku da koguna.
Kawo yanzu dai Ma’aikatan agaji na can na ci gaba da aikin ceto yayin da ake kokarin kawar da mutane daga gidajensu don gudun aukuwar wani karin mummunar al’amari.