Hukumar dake kashe gobara ta Jahar Kano, ta tabbatar da mutuwar wani Matashi mai suna Yusuf Aliyu, mai kimanin shekaru ashirin, inda ruwa ya tafi dashi a Danbare, Layin Bakar Lamba a Kano. Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Hukumar ta sanar da hakane, ta wani bayani da ya fito ta hannun mai kula da huldan jama’a, Alhaji Saminu Abdullahi a Kano, a ranar Asabar.
Yace “mun sami wani kira na gaggawa daga Danlami Danladi misalin karfe hudu saura kwata na yammacin ranar Juma’a.”
KARANTA:- Manchester City za ta ɗauki Jack Greelish, Arsenal na gabda kammala cinikin Madison
“Yake shaida mana cewar akwai wani Matashi wanda ruwa ya tafi dashi, Nan take bayan mun kammala wayar dashi muka tura jami’an mu da misalin karfe hudu da minti biyar.” kamar yadda ya bayyana.
Alhaji Saminu Abdullahi yace koda muka fiddo da Yusuf Aliyu ya rigaya ya mutu.
Yace nan take muka mika gawar ga mahaifinshi Aliyu Sufiyanu.
Alhaji Saminu Abdullahi yace ana cigaba da bincike don gano musabbabin aukuwar lamarin.
A wani labarin AHMED MUSA: Dalili na na barin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars
Dan wasa Ahmed Musa, yabar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars bayan share watanni uku, inda ya koma wata kungiyar kwallon kafa ta Fatih Karagumruk dake Kasar Turkiyya.
Adai ranar Alhamis ne Dan wasa Ahmed Musa ya kammala zama Dan wasan Fatih Karagumruk har na tsawo shekaru biyu bisa Yarjejeniyar kara shekaru nan gaba.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kammala zama Dan wasan Fatih Karagumruk yace ” na yi sha’awar zuwan kungiyar ta Fatih Karagumruk ne saboda kudirin su, da kuma kyakykyawan manufarsu.”
Ya cigaba da cewa ya shirya tsaf don ganin sauran abokanan wasan sa, su zo don su cigaba da baiwa Fatih Karagumruk gudummawa da iya karfin sa.
Kungiyar dai ta Fatih Karagumruk ta samu nasarar dawo wa babban rukunin kwallo na Kasar Turkiyya a kakar wasa ta 2019-2020 bayan ta share shekaru 35 ta neman haka.
Kungiyar ta Fatih Karagumruk suna cigaba da shirye-shiryen su inda za suyi wasan sada zumunci da kungiyar kwallon kafa ta Alanyaspor da Kasimpasa a ranar July 30 da August 5.