Ruwan sama mai sauka tare da guguwar iska Mai taanani ta lalata gidaje da dama na miliyoyin naira a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya, Wanda ya kasance ruwan sama na farko a wannan lokacin, ya fara sauka ne yan mintoci bayan karfe 3 na yammacin ranar Talata kuma ya dauki sama da sa’o’i hudu Yana sauka.
Ya lalata gidaje da dama na laka a yankin Maiduguri da wasu sassa na tsakiyar birnin ya bar mazauna garin da dama na Neman mafaka.
Wakilin Jaridar Daily Trsut da ya zagaya birnin ya ruwaito cewa guguwar ta lalata rufin gidaje da dama tare da tumbuke bishiyu a wurare da dama a cikin birnin Maiduguri da kewaye, lamarin da ya tilastawa jama’a kwashe tarkace da datti da sauran dukiyoyi da guguwar ta lalata.
Duk kokarin da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno SEMA ta yi, ya citura, amma wani ma’aikacin hukumar da bai so a bayyana sunansa ba ya ce jami’an hukumar sun fara tantance barnar da guguwar ta yi.