By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 11 ne aka tabbatar da mutuwarsu tare da lalata dukiyoyi a kasar Rwanda bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a sassa daban-daban na kasar a daren ranar Asabar, kamar yadda ma’aikatar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta sanar.
Dattijuwar Data Fi Tsufa A Duniya ‘Yar Kasar Japan Ta Kwanta Dama Tana Da Shekaru 119 A Duniya
Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun fito ne daga gundumar Nyamasheke da ke yammacin kasar Rwanda, yayin da uku kuma suka fito daga Kigali babban birnin kasar, kamar yadda alkalumman ma’aikatar suka nuna.
Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, sun mutu ne sakamakon zaftarewar kasa yayin da wasu kuma suka mutu bayan ruftawar gidajensu, a cewar ma’aikatar.
A wani lamari da ya faru, zaftarewar kasa ta rushe gidan wani magidanci, inda ta kashe ‘ya’yansa uku tare da raunata daya a gundumar Nyamasheke.
Ma’aikatar ta ce wasu mutane 13 a gundumomi daban-daban sun jikkata sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda kuma ya yi sanadiyyar rushewar gidaje sama da 100 a yankuna daban-daban.
Ana dai ci gaba da shirye-shiryen tallafa wa mutanen da abin ya shafa ta fuskar matsugunin gaggawa da kuma shirye-shiryen binne su.
Ya ce yayin da yake yin kira ga hukumomin yankin da su tabbatar da cewa mazauna wuraren da ake ganin akwai yankunan da ke da hatsarin gaske an mayar da su wuraren da ke da tsaro.
Ana sa ran kasar Rwanda za ta samu ruwan sama mai karfi daga ranar 21 zuwa 30 ga watan Afrilu, a cewar hukumar hasashen yanayi ta kasar. (Xinhua/NAN)
Comments 2