• Ruwan sama a jihar katisna ya kashe Mutum 2.
• Ya yin da ya yi sanadiyar lalacewar gine-gine 1,500 a jihar ta Katsina.
• Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa SEMA reshen jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Hukumar bada agajin gaggawa SEMA reshen jihar Katsina ta ce, gine-gine sama da dubu 15,000, saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar ya lalata, a ranar Litinin din da ta gaba.
Mai Magana da yawun hukumar Umar Mohammed ya bayyana cewa, Akalla kananan hukumomin uku ne lamarin ya shafa.
Muhammed ya kara da cewa, a yau Laraba cikin gine-gine 1500, gidaje 800 lamarin ya shafa. Inda ya hadar da kananan hukumomin Faskari, Bindawa da kuma karamar hukumar Sabuwa.
Kazalika ya ce, a karamar hukumar Bindawa, inda akasami ruwan saman da ya kwashe akalla awa biyar, ya yi sanadiyar mutuwar Mutum biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sabbin Lauyoyi Sun sha rantsuwar Kama aiki
Rahotanni sun nuna cewa, ruwan saman ya fara ne da musalin karfe 10 na safen ranar Litinin, Inda ya kai har musalin karfe hudu na yammaci, Wanda ya tilastawa masu motoci aje ababen hawan su.
Wasu mazauna yankin da lamarin ya shafa sun tattauna da Kamfanin dillancin labaran Nigeria NAN cewa, su na cikin damu wa matuka, sanadiyar toshewar hanyoyi da ruwan saman ya janyo.
Daya daga cikin matuka Mota da ke yankin Mai suna Muhammad Safana ya ce, lamarin zai iya kazanta, Indai dai ruwan saman ya cigaba da sauka.
Comments 1