Wani ruwan sama kaman da bakin kwarya ya kashe akalla mutane bakwai a Kasar Saudiyya.
Hukumar Tsaro ta farin kaya ta saudiyya ce ta tabbatar da afkuwar mummunan lamarin a yau. Inda ta ce an fara tsugaga ruwan ne tun ranar Juma’a, wanda kuma ba a tsagaita ba har zuwa ranar Lahadi a yankin Hafar Al-Baitin.
Ruwan saman ya halaka ababen hawa guda 40 tare da ruguza gidaje uku. Ya zuwa hada wannan rahoto, majiyar Jaridar Tantabara Hausa ta ce, har yanzu akwai mutane da ba a iya gano su.