Rundunar sojin ruwa ta bayyana wani rahoton da a ke yawo a kafafen yada labarai na zamani da ke cewa, rundunar ta fitar wani rukunin sunayen na musamman wato (supplementary), na wadanda zata dauka aiki a matsayin labarin “kanzon kurege”. Inda kuma ta gargadi wasu jaridun yanar gizo da su kare Martabar su.
Daraktan yada labarai na Shelkwatar rundunar Cdr Suleman Dahun ne, ya yi wannan gargadin, a cikin wata sanar da ya fitar jiya Litinin a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce, domin kauce wa jita-jita sunayen da ake yadawa na karya ne, Kuma badaga shelkwatar rundunar sojin ruwa ya ke ba.
Daraktan ya kuma shawarci al’umar Naijeriya da su nisanta kansu da wannan rukunin sunayen da ake yadawa, inda kuma ya ce, “Masu yaudaran mutane ne kawai, suka Kirikiri Wannan abu da ake yada wa, Kuma ya kamata yan Naijeriya su Kaurace mai, domin kaucewa kawo wani yamutsin addini
KARANTA WANNAN LABARIN: matsalar Tsaro Sarkin Musulmi da Malamai sunyi addu’o’i a Abuja
Kazalika ya ce, yanzu haka rundunar sojin ruwa, ta bakin kokarin ta, wurin ganin ta magance yaduwar irin wadannan labaran karyan.
A karshe Dahun ya shawarci dukkannin al’uma baki daya, da su ziyarci shafin yanar gizo na rundunar sojin ruwa, domin samun ingantaccen bayanai, kan aikin daukan sabbin jami’an da rundunar ta ke yi. Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran kasar nan NAN ya ruwaito.
Comments 1