Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa daga cikin kudaden da aka ajiye a wajen bankunan wato hannun jama’a, an samu nasarar karbo Naira tiriliyan 2.1 tun lokacin da aka fara shirin sake fasalin naira da babban bankin Najeriya ya bullo da shi.
Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani jawabi da ya yi wa ‘yan Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sake Fasalin Naira: Ina Son Hana Amfani Da Kudi Ne A Zabe – Buhari
“An sanar da ni cewa tun da aka fara wannan shirin, an samu nasarar karbo kusan Naira Tiriliyan 2.1 daga cikin takardun kudin da a baya ake rike da su a wajen tsarin banki.
“Wannan yana wakiltar kusan kashi 80% na irin waɗannan kudade. Don haka a takaice da matsakaici da dogon lokaci, ana sa ran za a samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki sakamakon koma bayan da aka samu na kudaden, da durkushewar ayyukan tattalin arziki na haram da zai taimaka wajen dakile cin hanci da rashawa da kuma samun kudi ta hanyoyin da ba bisa ka’ida ba, daidaiton farashin canji, samar da lamuni cikin sauki da rage kudin ruwa,” inji shi.
A wani labarin kuma, Ku Zabi ‘Yan takarar Da Kuke So Ba Tare Da Tsoron Kowa Ba – Buhari ga ‘yan Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi dan takarar da suke so a zabe mai zuwa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Buhari ya ce ‘yan kasar nan su yi zabe ba tare da tsoro ba.