Yayin da adadin wadanda ke kamuwa da cutar korona ke karuwa, wasu na warkewa a Jihar Legas, inda gwamnati ta ce ta sallami mutum 22.
Ya zuwa yammacin ranar Asabar, Leags ta tabbatar da samun mutum 1,022 da suka harbu da cutar, an sallami 225 daga cikinsu, 25 sun rasa rayukansu.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, 8 daga cikin 22 din mata ne, a yayin da 14 kuma maza ne.
An sallame su ne daga cibiyoyin killace masu jinyar cutar da ke Yaba da Luth da kuma Lekki.