Wata kyakkyawar budurwa mai diri da sura ta bayyana yadda kwastomomin abinci ta ke tahowa daga nesa don siyayya wurinta.
Matar mai suna Celestina Etornam, wacce aka dinga yawo da hotunanya a kafafen safa zumunta bayan kwanaki kadan da fara sana’ar abincin ta samu tsokaci daban-daban a kafafen sada zumunta.
KU KARANTA: Budurwa ta sharara wa saurayinta mari, ta ƙi karɓar tayin aurensa, ta buƙaci ya zage damtse
A wallafar ta ci mazan Ghana na kamo hanya daga nesa musamman don siyan abincinta.
Ta shaida yadda a baya take sayar da biredi wanda daga baya ta koma sana’ar abinci.
Ta ce asali kanwar babarta ce ke sana’ar, bayan ganin ta tsufa ne yasa ta amshi sana’ar hannu bibbiyu.
A wani bidiyo da wata @query996 ta wallafa, anga inda tace alaka mai kyau da kwastomiminta maza wadanda su ka dinga siyan abinci wurinta.
Da alamu ta san yadda ake kulawa da kwastomomi dakyau.
Budurwa ta tashi saurayi a Twitter bayan ya ce ya shirya aure amma babu matar aure
Wata mata a ranar Asabar, 26 ga watan Nuwamba ta tashi wani matashi a Twitter yayin da ya bayyana cewa yana da zone amma bai samu budurwar da zai nemi aurenta ba, LIB ta ruwaito.
Abin ya fara ne bayan wani kwararre a harkar soyayya ya bukaci wadanda su ka yi aure da su gabatar da hotunan aurensu.
Sai dai matashin ya wallafa hoton zobe a hannunsa inda yace na aure ne amma har yanzu be samu matar da zai aura ba.