A kwanakin baya ne dai fitacciyar jarumar finafinan Hausar nan da ta ci zamani a baya Ummi Zee-zee ta fito da wani salo da wasu kw ganin don a san da ita ne.
Cikin masu wancan hasashe har da abokin aikin ta a masana’antar wato Zaharaddeen Sani.
Cikin abinda Zee-zee ta faɗi shine irin halin da ya shiga har tasi kashe kanta saboda damfarar ta da wani Inyamuri ya yi, amma fa a cewar ta.
Wannan ne ya sa Zaharaddeen Sani fitowa ɓaro-ɓaro don yana kalubalantar ta da wancan kalamai tare da nuna cewa karya ne tsagwaronta.
To sai dai bayan nuna wa juna ɗan yatsa da Zee-zee suka yi da Zaharaddeen, daga bisani dai ƙura ta zo ta lafa, lamarin da ake gani tamkar haɗin baki tsakanin jaruman biyu.
A yanzu haka dai bayan shafe tsawon wancan lokaci ba a ji ɗuriyar Zaharaddeen da Zee-zee ba, yanzu haka ta sake fitowa ta yi wasu kalamai da ya ɗauki hankalin jama’a, inda take cewa ita kam ma ta tsani kwalliya a hoto wanda ake kira filter a turance.
Ta ce dalilin ta na yi haka kuwa shine lura da irin zubi da kuma diri gami da kyawun da Allah Ya hore mata, don hala babu ta yadda za ta sake yin wata kwalliya kuma.
Sai dai maganganun nata sun ja mata suka daga mabiyanta a shafin Instagram inda nn ne ta wallafa wannan bayanai, yayin da a hannu guda kuma wasu ke ta mata Ala-son-barka tare da jinjina mata bisa wannan ɗabi’a.
To ko ma dai menene yanz haka dai babu wani dan Masana’antar Kannywood da ya fito ya ce uffan dangane da wannan kalamai na Ummi Zee-zee, amma kamar yadda muka faɗi a baya, wasu lokutan jarumai irin ta na yin wani abun da zai ja hankalin jama’a don a ci gaba da tunawa da su tare da sanin cewa suna nan.