Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce za ta yiwa maza ‘yan kasar miliyan guda da rabi dake tsakanin shekaru 15 zuwa 49 kaciya a wani yunkuri na yaki da cutar HIV.
Wannan ya biyo bayan binciken da aka gudanar wanda ya nuna cewar maza sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar lokacin jima’i saboda rashin yin kaciyar.
Wata kungiyar agaji ta ‘Human Appeal Associates’ ta cimma yarjejeniya da ma’aikatar lafiyar kasar domin neman mutanen da ba a yiwa kaciyar ba, domin ganin sun mika kan su a musu nan da shekaru 5 masu zuwa.
Rahotanni sun ce a Jihohi 3 daga cikin Jihohi 10 da ake da su a Sudan ta kudu ne kawai ake yin kaciya, yayin da sauran yankunan ke kyamar ta.
Gwamnatin kasar ta bayyana rashin yin kaciyar a matsayin babbar barazana ga harkokin kula da lafiyar kasar, musamman wajen yaki da cutar HIV.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce a karshen makon da ya gabata, akalla maza 100 dake tsakanin shekara 15 zuwa 49 suka ci gajiyar wannan sabon shirin wajen gabatar da kan su a musu kaciyar.