Daga: wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Wani Farodusa Kuma Darakta a Masana’antar shirya finafinai ta kannywwod Aliyu Muhammad Haris ya gurfanar da Fitaccen jarumi Sadik Sani Sadik a gaban Kotun Shari’ar Muslumci dake Unguwar Hotoro ta jihar Kano bisa zargin da yake yi masa na karbar kudin sa daya yi bisa Alkawarin cewa zai yi masa aiki ya fito a matsayin Jarumi a cikin fim din sa.
Amma bayan sun kulla yarjejeniyar sai Jarumi Sadik Sani Sadik ya karya Alkawarin da aka yi da shi ya ki halartar zuwa wajen aikin kamar yadda aka tsara.
Bayan karya Alkawarin da Sadik Sani Sadik ya yi ba tare da ya bada wani gamshashshen uziri ba sai suka fara wasan buya tsakanin sa da Furodusa Aliyu Haris har ta Kai ga ganin sa ya yi masa wahala, Kuma ko ya Kira shi baya daga kiran wayar sa.
Don haka sai muka sauya shi inda muka maye gurbin sa da jarumi Ali Nuhu.
Duk wani kokari na ganin an daidaita tsakani Kan a samu maslaha Aliyu Haris yace ya bi domin a rabu cikin sauki Amma Hakan bai samu ba, domin a cewar sa “Na bi ta hanyar Usman Mu’azu da sauran masu fada a ji domin a samu warwarewa cikin sauki Amma Hakan bata samu ba.
Wannan tasa wata rana dana samu labarin yana Shifrayit muka je da ‘Yan Sanda sai dai munyi rashin nasar ba mu same shi a wurin ba.”
A yanzu dai Aliyu Muhammad Haris ya Kai karar Sadik Sani Sadik Kotun Shari’ar Muslumci dake Unguwar Hotoro a cikin garin Kano in da yake neman Kotun da kwantar masa da hakkin sa.
Har zuwa lokacin hada wannan labarin dai ba mu samu jin ta bakin Sadik Sani Sadik ba, don mun Kira wayar sa bai daga ba, Kuma mun aika masa da sakon Kar ta kwana ta waya bai ba mu amsa ba.