By Abbas Yakubu Yaura
Sabon babban sakataren hukumar jin dadin alhazai na jihar Bauchi ya karbi ragamar aiki a ranar Litinin 1 ga watan Nuwamban na shekara 2021,tare da yiwa gwamnan jihar alkawarin cire kitse daga cikin wuta.
Babban Sakataren hukumar, Malam Abdul-Rahaman Ibrahim Idris ya bada wannan tabbaci ne a yayin gudanarda kwarya-kwarayar taron karbar ragamar mulki wanda ya gudana a dakin taro na hukumar,inda ya bayyana mahajjata a matsayin bakin Allah wadanda ya kamata a bawa fifiko.
Malam Abdul-Rahaman Idris ya kara da cewa aikin Hajji na daga cikin ginshikan Addinin Musulunci guda biyar da suka wajaba akan kowane musulmi dake da Hali,sai dai kuma yayi kira ga masu ruwa da tsaki akan sha’anin aikin Hajji, da su bullo da wasu hanyoyi da zasu tallafawa maniyyata aiki Hajji wajen samun damar gudanarda ibada karbabbiya.
Kana ya bukaci goyon bayan Mambobi hukumar gami da shuwagannin da daukacin ma’aikatan hukumar da sauran masu fada aji na fannin domin samun nasarar gudanarda aikinsa cikin nasara, tare da nanata aniyarsa ta yin aiki tukuru ta kowace fiska dan ganin ya gudanarda aikinsa yanda ya kamata.
Tun da farko da yake nasa yawabin, shugaban hukumar jin dadin Alhazan kana babban limamin Bauchi Imam Bala Ahmad, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yi kyakkyawan zabi ta kuma sanya kwarya a gurbinta, wajen zakulo babban Sakataren.
Ya kuma bayyana cewa nan bada jumawa ba jihar Bauchi za ta zama uwa mabada mama a bangaren gudanarda aikin Hajji.
Sannan ya bukaci sabon Babban Sakataren daya rika tambaya akan duk wani abunda ya shige masa duhu wanda ya zama wajibi,sa’annan ya yi masa fatan Alkhairi tare da yimasa Addu’ar Allah ya yi masa jagora a yayin gudanarda aikinsa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Daraktan Mulki na hukumar Malam Alkasim Danlami Shall ya taya Malam Abdul-Rahaman murnar samun sabon mukamin,tare da bayyana mukamin sabon Babban Sakataren hukumar jin dadin Alhazai na jihar Bauchi a matsayin wata babbar tagomashi da Allah ya bawa hukumar,inda ya bashi tabbacin cewa daukacin ma’aikatan hukumar zasu zama masu biyayya da da’a a gareshi.