Gwamnatin Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da ke tafiye-tafiye zuwa Wuhan a China da su kaucewa mu’amala da mutanen da ke nuna alamun rashin lafiya.
Gwamnatin ta yi wannan gargadi ne sakamakon bullar kwayar cutar Coronavirus wadda ta samo asali daga birnin na Wuhan.
A shafinta na Twitter, gwamnatin ta bukaci mutane su guji kusantar dabbobi masu rai ko mara rai da kuma kasuwannin dabbobi.
Gwamnatin ta ce ma’aikatar lafiya ta hannun hukumar dakile yaduwar cututtuka da sauran hukumomin lafiya na kara kaimi wajen dakile barkewar cutar a sassan kasar.
A cewarta, hukumar dakile bazuwar cututtuka na yin nazari kan illar shigo da kayayyaki daga wasu kasashen zuwa Najeriya.
Hukumar kuma tana tatatunawa da hukumar lafiya da duniya WHO, kan yadda za a shawo kan lamarin.