Wakilinmu Shu’aibu Ibrahim Gusau
Sabon gwamnan jihar zamfara Hon. Bello Matawallen Maradun, ya bayyana cewa ya maida matasa 1400 aiki, wadanda Gwamnatin Baya ta Kora a lokacin Milkin ta.
Sabon gwamnan ya bayyana hakan ne cikin Jawabinsa da ya gudanar gurin karbar rantsuwa Jim kadan Bayan Kammala Rantsar da Shi a Matsayin Gwamnan Jihar Zamfara.
Idan ba’a mantaba su dai wadannan matasan gwamnatin Abdul’aziz ce ta daukesu aiki Kuma daga bisani ta dakatar dasu kusan shekaru hudu da suka wuce.
Bisa wannan dalili ya Sanya zababben Gwamnan yace ya maidasu aiki ne Tare da Bincikar Abun da ya Faru a Baya.
Kuma Hon. Bello ya ja kunnen masu daukan mutane da sunan tantancewa, su kula domin Gwamnatinsa Gwamnatin kowa da kowa ce, Inji shi.