Akalla mutane tara ne suka mutu, biyar suka jikkata, yayin da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da wasu dabbobi a wasu sabbin hare-hare da aka kai a jihar Kaduna.
Al’ummomin da abin ya shafa dai na cikin kananan hukumomin Igabi da Zariya a jihar.
Jami’an tsaro sun kuma kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a karamar hukumar Igabi.
Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya bayyana cewa, rahotannin da jami’an tsaro suka samu sun nuna cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen Sabon Birni da wani matsugunin makiyaya a yankin Rigachikun, dukkansu a karamar hukumar Igabi inda suka harbe wasu mutanen kauyen bakwai har lahira.
A cewar Kwamishinan, mutane hudu kuma sun jikkata, yayin da aka ce an yi awon gaba da awaki, tumaki da sauran dabbobi.
Har ila yau, ‘yan bindigar sun kai hari a wani matsugunin makiyaya da ke Barebare, a karamar hukumar Zariya, inda suka kashe mutane biyu, suka kuma raunata wani sannan suka yi awon gaba da dabbobi.
A wani labarin kuma jami’an tsaro sun kashe wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a kauyen Kerawa da ke karamar hukumar Igabi.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa an kashe su ne a lokacin da sojoji suka tare su tare da fatattakar su a dajin Malul bayan wata arangama da suka yi.
An samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 na barayin.
Dimokuradiyya ta rawaito Gwamna Nasir El-Rufai ya yabawa sojojin bisa gaggawa da suka yi tare da mika ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe.
TVCNEWS
Comments 1