A safiyar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyukan dake kananan hukumomi uku a jihar Benue inda suka kashe mutane 25 tare da raunata wasu da dama.
Wani mazaunin yankin, Mista Tewase Hembe, wanda ya zanta da DAILY POST ta wayar tarho, ya ce kananan hukumomin guda uku sun hada da Guma, Logo da kuma Tarka.
Ya ce karamar hukumar sa ta fuskanci mummunar harbe-harbe a tsakanin karfe 9 na daren ranar Litinin zuwa karfe 4 na safiyar ranar Talata, inda aka samu gawarwaki 15 a yankin Tyotugh da ke karamar hukumar Tarka yayin da wasu gawarwaki tara aka tsinto daga Guma da daya, wani basarake daga Logo.
Ya ce an ci gaba da neman karin gawarwaki tare da fargabar adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.
Caleb Aba Shugaban Karamar Hukumar Guma, wanda ya tabbatar wa DAILY POST faruwar lamarin, ya ce an kashe mutane bakwai a wani samame da aka yi a kauyen Tse-Sumaka da ke kusa da Reshen Umenger a gundumar Mbadwem na Guma.
Har ila yau, mai baiwa gwamnan jihar Benue shawara kan harkokin tsaro, Laftanal Kanal Paul Hemba (Mai ritaya), ya ce adadin wadanda suka mutu ya zuwa yanzu zai iya haura 25 yayin da ake ci gaba da Neman wadanda suka bata.
Jami’ar hulda da jama’a ta ‘yan sanda (PPRO), SP Catherine Anene, ba ta amsa kiran wayarta ba, kuma ba ta amsa sakon tes da aka aika mata ba.