Yan bindiga, a yammacin ranar Alhamis din da ta gabata, sun kashe a kalla shanu 10, tare da jikkata wasu 23 a kauyen Waren, dake karamar hukumar Riyom na jihar Filato.
Sakataren kungiyar Miyetti Allah na Kasa MACBAN, Abdullahi Yusuf Ibrahim, ne ya tabbatar da afkuwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce, sun kai karar lamarin zuwa hedikwatar rundunar yan sanda ta Riyom, da kuma sashi na 6 na Rundunar Operation Safe Haven donmin tabbatar da zaman lafiya a yankin baki daya.
Sai dai kungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaro da abin ya shafa, na karamar hukumar Riyom da gwamnatin jihar, da su zakulo wadanda suka aikata wannan aika -aikar, tare da biyansu diyyar asarar da aka samu sanadiyar harin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnan jihar Legas ya rattaba hannu kan dokar Haraji
Ko da mane ma labarai suka tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, har kawo hada wannan rahoton, bai biyo bayan kiran wayar da akayi mashi ba, kuma bai amsa sakon kartakkwana da wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya tura mishi ba.
Comments 1