Rahotannin da ke shigowa a halin yanzu shi ne; rundunar Sojin saman Nijeriya. NAF ta karɓi jirginta na biyu mai saukar ungulu ƙirar Mi-171E da gwamnatin tarayya ta saya daga ƙasar Serbia.
A wani saƙo da NAF ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa wannan ne jirgi na biyu mai saukar ungulu ƙirar Mi-171E da gwamnatin tarayyar ta saya.
Rundunarta bayyana cewa wannan ne jirgi na 23 da rundunar ta saya tun a 2015.