Cire Mai Mala Buni a matsayin Shugaban Kwamitin Ruƙo na Jam’iyyar APC, wasu Gwamnoni suka hura wutar kamar yadda Majiya ta bayyana.
Duk da ana cikin ruɗanin cewa an kori Buni daga Muƙamin sa, wasu Majiyoyi mai ƙarfi sun shaidawa Jaridar Daily Trust cewa, wasu Gwamnoni ne suka rura wutar tsige Gwamnan Jahar Yobe a ranar Alhamis a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-yanzu: Kotu Ta Kori Gwamnan Ebonyi, Mataimakinsa Kan Sauya Sheka Ba Bisa Ka’ida Ba
Majiyoyin sun ce bayan zuga korar Buni Gwamnonin da suka haɗa da na Ekiti, da Jigawa, da Filato, da Kebbi, da Niger, da Kaduna sunyi taro da Shugaban Ƙasa a ranar Asabar, inda suka nemo iko domin korar Buni a matsayin Shugaban Kwamitin Ruƙo na Ƙasa.
Ɗaya daga cikin Majiyar, Gwamna daga Kudu ya shaidawa Daily Trust cewa yaje taron, inda Buhari ya bada umarnin a cire Buni a matsayin Shugaban Jam’iyyar.
“Sanarwar dake cewa sauke Shugaban Kwamitin Ruƙo da Shugaban Ƙasa yayi ba gaskiya bane, abun dariya ne, domin ina a wajen, a lokacin da Shugaban Ƙasa ya bada umarnin a cire Gwamanan Yobe,” inji shi.
Yace Gwamnan Niger an bashi umarni yayi taron Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa.
Wata Majiya daga Villa tace Gwamnonin sun bayyana matsayar su na cire shi, sakamakon Buni bashi da niyyar shirya zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar na Ƙasa.