Wani gajeren bidiyo ya bayyana yadda aka kera kayan amfanin cikin wani gida wanda su ka yi matukar daukar hankulan mutane da dama, Legit.ng ta ruwaito.
An wallafa bidiyon ne a TikTok wanda mutane da dama su ka sha mamaki kan yadda aka yi amfani da kankare da tayis wurin kawata su.
KU KARANTA: Majalisar Akwa Ibom ta ayyana kujerun ‘yan majalisar biyu a matsayin wadanda babu kowa
Duk da dai wasu na ganin lamarin ya zama shirme, amma wasu kuma sun kalli lamarin a matsayin fasaha ta musamman wacce ba a taba irinta ba.
Wasu kuma su na ganin wannan dabara ce ta musamman saboda ba za su taba lalacewa ba matukar ana kulawa dasu yadda ya dace.
Yadda ƴan zaman makoki su ka sace kujerun da matashi yayi haya don taron birniyar mahaifiyarsa
Wani Udam Samuel Aswear daga Jihar Binuwai ya koka akan yadda ‘yan zaman makoki su ka sace kujeru bakwai wadanda ya yi hayarsu don birniyar mahaifiyarsa a ranar Asabar, 12 ga watan Nuwamban 2022, LIB ta ruwaito.
Kamar yadda yace:
“Ka je biriniyar mahaifiyata kuma an sace kujeru 7 cikin wadanda aka aro, hakan yasa sai da na biya N25,200 (ko wacce kujera 3,600)” kamar yadda ya rubuta ranar Litinin.”