Gwamnan Jahar Gombe Muhammed Inuwa Yahaya yace zamu cigaba da samar da Makarantu daf da gidajen jami’an tsaro matukar barazanar diban Dalibai zai cigaba .
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana haka ne ga manema labarai a Abuja bayan kammala tattaunawarsa da Farfesa Ibrahim Gambari a ranar Litini. Kamar yadda jaridar Dailytrust ta wallafa
“Mun samar da wata hanyar taimakawa don yin karatu a makarantu ta hanyar samar da Yan banga da mafarauta don kula da Makarantun mu.”
KARANTA:- Da zafinsa: PDP ta bukaci kotu ta tsige Gwamnan Zamfara da mataimakinsa
“Abunda ma yafi kowane a fannin tsaron makarantu shine, zamu fara gina manyan makarantu wanda za su diba Dalibai da yawa kusada gidajen jami’an tsaro, Wanda hakan zai sa ba za’a sanya daliban cikin hatsari ba tunda suna kusa da Jami’an tsaro.”
“Wannan zai kawo mana zaman lafiya a cikin makarantunmu, Kuma makarantu a Jahar Gombe za su samu tsaro ingantacce, Kuma muna fatan Allah ya taimake mu a kan haka.” Kamar yadda Yahaya ya bayyana.
Jahar Gombe ta hada iyaka da jahohi biyar wanda rashin tsaro yayi kakagida a jahohin, wannan ya kawo tashin hankali a Jahar ta Gomben.
“Amman munyi saurin daukar matakai da suka kamata, kuma za mu cigaba da kokari akan haka., Duba da Sarakuna da jagororin Al’umma da kuma sauran Yan banga da Sakai na kokarin kara hada kawunansu.”
“Ahakan ina iya cewa jahar Gombe ta zaune lafiya sama da sauran jahohin, Kuma muna matukar godiya ga Allah da ya hada kan Mutanen mu.”