An rantsar da Anthony Albanese a matsayin sabon shugaban kasar Australia kuma zai halarci taron kasa da kasa batare da bata lokaci ba.
Jam’iyyar Labour ta Mista Albanese ta doke gwamnatin mazan jiya ta Scott Morrison a zaben da aka gudanar a ranar Asabar.
Har yanzu dai babu tabbas ko Mista Albanese zai samu rinjaye ko kuma zai yi mulki tare da goyon bayan ‘yan adawa.
Faraministan ya Kuma tafi Tokyo a ranar Litinin don ganawa da shugabannin kasashen da ake kira Quad, da suka hadar da Amurka, Indiya da kuma Japan.
Tun da farko dai an rantsar da shi tare da wasu manyan jami’an majalisar ministocisa guda hudu, da suka hada da sabon ministan harkokin wajen kasar Penny Wong wanda suka tafi tare zuwa kasar Japan domin halartan taron.
A wani labarin Kuma na daban.
Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Dasuki, Bafarawa, Yuguda, bisa zargin karkatar da kudi Naira Billiyan 388
A ranar Litinin ne gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA, Kanal Sambo Dasuki, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da kuma tsohon karamin ministan kudi, Bashir Yuguda, a gaban kotu bisa zargin cin hanci da rashawa.
An sake gurfanar da su a wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja bisa zargin su da cin amana da almubazzaranci da dukiyar al’umma da suka kai Naira biliyan 388.
A tuhume-tuhume 16, Dasuki, Bafarawa da Yuguda, an zargi su da karkatar da kudade daban-daban a wasu kudade zuwa asusun banki daban-daban bisa zargin karkatar da kudaden da aka ware wajen sayo kayayyakin Samar tsaro a kasar nan.
Laifukan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC ta shirya, sun yi ikirarin cewa, an yi amfani da kudaden ne wajen yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2015.
Lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen, duk wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Biyo bayan wani roko da wani babban Lauyan Najeriya SAN, Prince Lateef Olasunkanmi Fagbemi ya yi, mai shari’a Halilu Yusuf ya amince da belinsu da aka ba su tun a shekarar 2018 a lokacin da aka fara gurfanar da su a gaban kuliya.
Alkalin ya tsayar da ranar 7 ga watan Yuni shekarar 2022 domin cigaba da Saura ran karar.