A wannan rana ta Asabar za a fara fafata sabuwar kakar gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙwallon ƙafa guda 20 inda daga ciki za a sami zakara a cikinsu a ƙarshen kakar wasa ta bana wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.
A kakar wasan data gabata dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ce ta zamo zakara bayan da ta lashe gasar da maki 99 inda rabonta data lashe gasar shekaru 30 kenan kuma ta lashe a ƙarƙashin haziƙin mai horas wa wato Jurgen Klopp.
Sai dai a wannan sabuwar kakar wasan da za a shiga kusan ko wacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta yi gyara da cefane mai kyau ta yadda bazata samu naƙasu ba a gasar.
A wannan sabuwar kakar wasan da za a fara tuni mai horas da ƙungiyar Liverpool wato Jurgen Klopp ya bayyana cewar bana ma Liverpool ta shirya domin sake lashe wannan gasa karo na 20 kenan tunda sun ɗanɗana sunji yadda take.
Shin ko wacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ce zata zamo zakara a kakar wasa ta bana ganin yadda manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa kamar su Chelsea da Manchester City da Manchester United da Arsenal da Liverpool da Tottenham da Everton da dai sauransu suke ganin zasu iya lashe gasar.