By Abbas Yakubu Yaura
Sabuwar majalisar ministocin Jamus zata kasance maza tara da mata takwas bayan Olaf Scholz, magajin Angela Merkel a matsayin shugabar gwamnati, ya nada sabbin ministoci 17 na gwamnatin kawance a ranar Litinin.
Scholz dan siyasar Jam’iyar (SPD) ya gabatar da mata hudu da maza uku a jam’iyar SPD,da kuma jam’iyyar FDP mai ra’ayin kasuwanci tana da maza uku da mace daya, yayin da Greens suka sanya mata uku da maza biyu.
Don haka majalisar za ta kunshi mata takwas da maza takwas masu rike da mukaman minista, yayin da Scholz shine shugaba wanda hakan zai sauya ma’auni kadan don nuna goyon baya ga maza.
Tun kafin zaben na watan Satumba, shugaban SPD yace zai sa aniyar samun daidaito tsakanin maza da mata a majalisar ministocin kasar nan gaba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa mista Scholz yace “Majalisar ministocin da ni ke jagoranta a matsayin shugabar gwamnati zata ƙunshi akalla rabin mata,”wanda Scholz ya wallafa a shafinsa na tweeted shekara guda data gabata.