Gwamnan Jahar Lagos Mr Babajide Sanwo-Olu ya shawarci mazauna Jahar Lagos da su guji duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kawuna, sannan su zamanto masu soyayya ga junan su, ta hanyar yabawa da gudunmuwar kowa da kuma Jahar a shekarar data gabata.
Sanwo-Olu ya bayyana haka a cikin saƙon shi na murnar shiga Sabuwar Shekara, wanda sanarwar Sakataren yaɗa labarun shi Mr Gboyega Akosile ya fitar, a cikin rana ta farko ta shekarar 2022.
Gwamnan ya kuma taya ƴan Legas da ƴan Najeriya murnar shaida sabuwar Shekara, yana mai cewa babu wata kyauta da Allah zai yi maka irin tsawon rayuwar ka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hatsarin Mota: Ana Fargabar Mutane Da Dama Sun Mutu A Hanyar Abakaliki-Enugu
Yace ” a madadin iyalai na da Gwamnatin Lagos, ina taya ƴan Najeriya musamman ƴan Legas, murnar shiga sabuwar shekara ta 2022.
A cewar sa duk da irin wahalhalun da aka sha wanda cutar Covid-19 ta janyo na taɓarɓarewar tattalin arziki, amma Jahar tayi namijin ƙoƙari wajen samar da gine-gine a Makarantu da mahalli da sauran su, baya ga haka, Gwamnatin ta cika alƙawurra da dama da ta yiwa Al’ummar Jahar, wanda ya taɓa rayuwar su kai tsaye.
Gwamna Sanwo-Olu ya jaddada cewa ” a shekarar 2022, gwamnatin sa zata maida hankali wajen cika alƙawurran data ɗauka domin ciyar da Lagos a matakin gaba ta hanyar Kasafi dana yi wanda na sanyawa hannu ya zama doka. Ƴan ƙasa zasu shaida ginin Makarantu, Asibitoci, hanyoyi da inganta tsaro da jindadin su.