Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ayyana ranar Litinin 2 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin murnar shiga sabuwar shekara na Musulunci na 1441. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da babban Sakataren gwamnati, Malam Abubakar Shekara ya sanyawa a hannu a ranar Lahadi, inda ya ce gwamnan ya ba da hutun wannan ranar domin a bai wa Musulmi damar murnar shiga sabuwar shekarar.
Tambuwal ya taya al’ummar jihar Sakkwato baki daya murna, sannan ya shawarce su da su yi amfani da wannan damar wajen gudanar da addu’o’in wanzar da zaman lafiya a fadin jihar da ma kasa baki daya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa; Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Lahadi a matsayin ranar 1 ga watan Muharram ta shekara 1441 bayan hijirar Manzon Allah (S).