By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro da su kara kaimi wajen sanya ido da kuma sintiri a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis bayan kammala taron kwamitin tsaro na kasa a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Aregebesola ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta gamsu da zaben gwamna da aka kammala kwanan nan a jihar Anambra inda dan takarar jam’iyyar APGA Charles Soludo ya zama zababben gwamna.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito A cewarsa, “An hada ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin kara sanya ido, wajen yin sintiri da kuma bin diddigin masu aikata laifuka, sannan kuma ba maganar iya Abuja-Kaduna kadai ba, harda sauran hanyoyin kasar nan.
“Eh, an tattauna kan hanyar Abuja-Kaduna musamman, amma mun yaba da yadda muke cikin lokacin bukukuwa.Don haka dukkan hukumomi sun himmatu wajen samar da tsaro ga Najeriya da kuma tabbatar da doka da oda.
Ministan yace hukumar ‘yan sanda ce kan gaba a harkar tsaro a cikin gida. Don haka kiyaye doka da oda zai fara ne da ‘yan sanda sannan a mika shi ga sauran hukumomin tsaro.
Da yake jawabi, Aregbesola yace an bayar da takamaiman umarni ga dukkan hukumomin tsaro.sannan yace ‘yan Najeriya su sa ran ganin an samu ingantacciyar amsa ga duk masu kalubalantar ’yancin Najeriya ta kowace fuska.
“Majalissar a yau ta dauki kwakkwaran mataki kan abin daya kamata a yi kuma ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa umarnin da shugaban kasa da kwamandan rundunar soji suka yi a yau, za a samu ingantacciyar amsa ga duk wani nau’in aikata laifuka a kowane bangare na Najeriya,
Kafin a fara taron, shugaban kasar ya yi wa mataimakinsa Laftanar Kanal Yusuf Dodo sabon mukaminsa na Kanal.
Kazalika wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,Farfesa Ibrahim Gambari, Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro,Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor.