Dan wasan gaba na Super Eagles na Najeriya, Sadiq Umar, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan watan Fabrairun 2022 a gasar na biyu na kasar Sipaniya.
Dan wasan ya yi fice a kulob dinsa a watan Fabrairu, inda ya ba da gudummawar kwallaye bakwai ( kwallaye biyar da ci biyu) a kulob dinsa na Almeria a wasanni hudu na gasar.
Dan wasan mai shekaru 25 ya taimaka wa Almeria ta samu nasara sau hudu a jere a cikin watan, wanda hakan ya sanya ta shiga cikin fafatawa a gasar zuwa rukunin farko.
Tsohon Dan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Partizan Belgrade wanda ya lashe kyautar ne a kan kudin kungiyoyi irinsu Huesca’s Jaime Seoane da Jose Corpar na SD Eibar.
Ya ci kwallo 20 a kakar wasan bara duk da cewa bai fara kakar da Almeria ba.
Amma yana fatan ya zarce haka a kakar wasa ta bana bayan ya zura kwallaye 13 tare da bayar da taimako bakwai a wasanni 25 da ya buga a gasar ta bana.
Sadiq Umar ya na daya daga cikin jerin sunayen ‘yan wasan Super Eagles da za su fafata a wasan Neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su yi da Ghana a karshen wannan watan kuma ‘yan Najeriya za su zuba ido su ga dan wasan ya maimaita irin nasarorin da ya samu a kungiyar ta Super Eagles.