Rahotanni dake fitowa daga Ingila na nuni da cewa; kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dake buga gasar Firimiyar Ingila, ta kammala siyen Timo Werner daga kungiyar Leipzig dake buga gasar Bundesliga ta Jamus, inda a halin yanzu zai koma Stamford Bridge a watan Yuli.
Werner ya koma Leipzig daga Stuttgart a 2016 inda ya ci kwallo 32 a dukkan fafatawar da ya yi a kakar wasan bana.
Dan kwallon shi ne na biyu da Chelsea ta siya don shirin tunkarar kakar tamaula ta badi, bayan dan wasan Ajax, Hakim Ziyech da ta sayo a watan Fabrairu.
Bayanai na nuni da cewa; Werner idan ya koma Chelsea a watan gobe ba zai buga wa RB Leipzig gasar kofin zakarun Turai ba da za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe a cikin watan Agusta ba.