Wata yarinya yar Shekara 15 dake aji biyu a Karamar Sakandire, ta yiwa Babbar Kotun Tarayya dake Kubwa Abuja bayani, yadda makwabcinta Dan Shekara 23 Prosper Iloh ya rika bata kwaya yana mata fyade.
Matashiyar wadda ke zaune a Dakwa Dei-dei Abuja, ta bada shaida a shari’ar da ake gudanar wa, kamar yadda lauyan dake shigar da kara Adamu Musa ya bukata.
Tace “Ina kan hanya zuwa coci, a lokacin da wanda ake kara ya gayyace ni gidansa a ranar 12 ga watan juli na Shekarar 2020. Sai naki zuwa, kuma na gaya mashi cewa ina kan hanyata, ta zuwa coci amma ya shawo kaina na bishi zuwa gidan sa, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun hallaka Dan Sanda, yayin da suka afka wani Otel a Abuja
“Mun tafi a saman mashina guda biyu, inda muka isa a Madala dake Suleja Jahar Niger, sai muka hau mota, muka bi kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
“Mun shiga gidan sa, sai ya kawo man lemun ‘fearless’, kuma ya sanya wani abu a ciki, kasancewar ina shansa, sai na kasance banda karfi.
“Abunda zan iya tunawa shine ya cire mani rigar mama, ya yi mani fyade. Nayi kokarin kururuwa amma sai ya kulle mani baki da hannun sa.
“Lokacin da ya kammala, sai ya dauke ni zuwa dakin giya, ya bani Ogogoro, amma duk da haka sai naji duk na gaji. Daganan ya kara kaini gidan sa, ya sake yi mani fyade a karo ba biyu
Ta kara da cewa, a lokacin da ta koma gida sai ta sanar da iyayen ta abunda ya faru, sai suka kai lamarin a ofishin Yan sanda.
Ta bayyana cewa yan sanda sun kaita Asibiti, inda aka yi mata magani, inda ta kara dacewa, tana da shekaru 13 a lokacin da lamarin ya faru.
A lokacin da lauyan dake kare wanda ake kara Celestine Mbam-Okeh ya yi mata tambaya, akan yadda ta san ya sanya ta magani a ciki, alhalin ba’a taba jima’i da’ita ba.
A maida jawabi, yarinyar tace a lokacin da tasha”fearless” shiyasa taji gajiya, don haka tayi tunanin akwai magani a ciki.
Bayan sauraron dukkanin jawaban su, Mai Shari’a Kezziah Ogbonnaya ya daga Shari’ar zuwa 8 ga watan Nuwamba domin cigaba da sauraron Shari’ar.
Comments 1