Sai da na Gargadi Aregbesola kan harin da za’a kawo wa Gidan Yarin Kuje — Sadiq
Dr Sadiq Amali Malami a Sashen Nazarin Zaman ta kewa na Jami’ar Tarayya ta Jigawa, ya bayyana cewar sai da ya gano za’a kai hari a gidan yarin Kuje.
A lokacin da yake jawabi akan harin a gidan Talabijin na Channels a cikin shirin Sunrise Daily a ranar Alhamis, Dr Amali yace ya rubuta wa Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola, akan kaiwa wurin hari.
KARANTA WANNAN LABARIN: Damfara: Kotu ta ɗaure Hafsan Soji na Boge daya ƙware wajen kwaikwayar sa hannun Buhari, Obasanjo shekara 7
Ƴan bindiga da aka yi amanna cewa ƴan Ta’adda ne, a ɗaruruwan su, sun kai hari a gidan yarin a daren ranar Talata.
Maharan sun yi amfani da Bam domin samun shiga can cikin gidan da kuma ta hanyar katangar gidan.
Kimanin Fursunoni 879 suka tsere daga gidan yarin a lokacin kai harin, inda ake kyautata zaton 70 daga cikin su mambobin Ƙungiyar Boko Haram ne.
Masana Harkokin Tsaro sun ce idan har ba’a ɗauki mataki ba daga Hukumomi ba, to za’a cigaba da kai harin.
“Ina da Kyakkyawar alaƙa da Ministan Cikin Gida da Kwanturola-Janar akan yawaitar kai hare-hare a gidan yari a Ƙasar.
“Naga wannan. Kuma wannan bashi ne karo na farko ba da lamarin ya faru, kuma abin baƙin ciki ne ba lallai wannan shine na ƙarshe ba.
“A lokacin da suke rage yawan mutane a lokacin cutar Covid-19, na shawarci Ministan Cikin Gida akan matakan da zasu ɗauka, da kuma illolin da rage yawan yake dashi.
“To idan Fursunonin daka saki suka haɗa kai da wasu a cikin Al’umma suka dawo domin sakin ƴan uwan su dake garƙame.
“Naga harin na zuwa, kuma ya ɗauki mataki, amma matakan tsaron sun yi kaɗan.