Wani matashi ɗan Najeriga ya koka kan takardun kuɗin da aka bashi lokacin da yaje ciro kuɗi a banki.
A cewar matashin, tarin ƴan naira biyar (N5) kawai aka lafke shi da su lokacin da yaje wani reshen bankin sa domin ciro kuɗi. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Allah ya yiwa sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi II, rasuwa
A wani bidiyo da ya sanya a TikTok, an ga matashin yana ta ƙorafi riƙe da bandir ɗin ƴan naira biyar a hannun sa.
Ba a san adadin ko nawa matashin ya ciro ba, amma an ganshi a cikin bidiyon riƙe da bandir 8 na ƴan naira biyar.
Yace bankin sa ne ya bashi kuɗin wanda hakan na nuna cewa babu manyan kuɗaɗe a bankin da yaje.
Ƴan Najeriya na matuƙar shan wahala wajen samun yin amfani da sababbin takardun kuɗin N200, N500 da N1000 waɗanda aka fito da su.
Wani mai amfani da sunan @storymustchange55 a manhajar TikTok ne ya sanya bidiyon.
Ta Mori Miji: Wata Budurwa Ta Fashe Da Kuka Bayan Ganin Irin Sha Tara Ta Arziƙi Da Mijinta Yayi Mata
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya gigita matarsa da ƙayatattun kyaututtuka waɗanda duka sanya ta zubar da hawaye
Wani matashin ɗan Najeriya ya nunawa sauran mazaje yadda yakamata ace suna yabawa matan su a ranar murnar zagayowar ranar haihuwar su.
Wani bidiyo wanda wani mai amfani da sunan @nesta_surprise8 a manhajar TikTok ya sanya, ya nuna lokacin da matashiyar matar tasa ta fashe da kuka saboda irin ɗimbin kyaututtukan da mijin nata yayi mata.