Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa’I ya sanar da kawo karshen tsarin karatun Almajirci a daukacin jihar, matakin da ya ce shi ne daukacin gwamnonin arewacin Nijeriya suka cimma matsayar dauka ke nan.
Yayin wata zantawa da kafar Talabijin ta Channels TV, El Rufa’i ya kuma ce tuni nazari ya yi nisa kan samar da wasu dokoki da kuma sauya fasalin wadansu, domin tabbatar da cewa, tsarin karatun na almajirci bai sake farfadowa ba a jihar kamar yadda Rfi Hausa suka nakalto.
Gwamnan Kaduna ya ce a halin da ake ciki gwamnatinsa ta yi nasarar mayar da Almajirai sama da dubu 30 zuwa jihohin da suka fito.
A baya-bayan gwamnonin jihohi a Nijeriya musamman a Arewa sun yi ta musayar maida almajirai zuwa ainihin garuruwansu, kuma bulllar annobar ta karfafa shirin da wasun su suka ce dama suna shirin aiwatarwa na kawo karshen tsarin karatun almajiranci, matakin da zai magance matsalar barace-barace da kananan yara ke yi akan tituna da layukan unguwanni.