Sai Mun Kawo Karshen Safarar Mutane, Alkalin Alkalai
Jaridar Thisday sun ruwaito Akingbolahan Adeniran Alkalin Alkalai na Jahar Ogun yace “Samar da Jami’ai na musamman Dan dakile safarar Mutane abune mai matukar muhimmanci a Jahar Ogun.”
Adeniran ya bayyana hakane a wani taron karawa juna sani da aka gabatar na kwana daya dakin taro na makarantar kimiyya da fasaha dake Abeokuta babban birnin Jahar.
KARANTA:-Bamu Shirya Karbar Yan Gudun Hijira Miliyan 240 ba Idan Najeriya ta wargaje
Kwamishinan yace hadin guiwa tsakanin Jami’an tsaro da kungiyoyi masu zaman kansu da wasu manyan hukumomin kadai zai kawo karshen safarar Mutane dake addabar yankin.
Mista Olamiden Mustapha mai ba gwamna shawara ta fannin tsaro yace hada kai da masu kafa doka da bullo da hanyoyi tare da wayar ma mutane kai kan illar shine zai rage wannan barnan.
Yace ” Yanzu da Kungiyoyi masu zaman kansu suka shiga cikin jami’an tsaro tabbas wannan ta’adin zai rage, sannan ya zama dole wajan koyar da maaikatan salo da dabara wajan kawo karshen safarar Mutane ba tare da an raunata wasu ba.