Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC na riko, ya bayyana cewa mafi yawan barayin Nijeriya suna boye ne a kasar Ghana.
Magu ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a Abuja, inda ya ce hukumar na tatttara bayanai wuri guda domin dawo wa da kudaden Nijeriya da aka sace aka jibge a kasar ta Ghana.
Shugaban EFCC din ya bayyana hakan ne a yayin da tawagar CIPRMP suka kai masa ziyara a hedikwatar hukumar.
A cewarsa, EFCC din tana hada hannu da takwararta na Ghana kan kudaden Nijeriya dake kasar domin tsara yadda za a dawo da su.