Babban Sufeto Janar na Yan sanda, Usman Alkali Baba, ya dauki matakin dakatar da masu garkuwa da mutane dake addabar jama’a a hanyar Legas zuwa Ibadan. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
A ranar Talata ne dai rahotanni suka ce sefeton yan sandan ya karbi bayanai daga kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin Ogun da Legas da kuma Oyo kan matsalar tsaro a hanyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Osinbajo bai halarci taron gangamin yaƙin neman zaɓen APC, Yayi wasu jawabai
Sakamakon haka, IGP ya fadawa majiyar Dimokuradiyya cewa, ya fahimci cewa, “ya ba da umarnin sake fasalin tsare-tsaren tsaro a kan babbar hanyar.”
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi ya fitar, ya ce an dauki matakin ne domin samar da isassun jami’ai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a kan hanyar da kuma dakile satar mutane da sauran munanan abubuwa.
A cewar Adejobi, IGP din ya jaddada cewa hukumar ‘yan sandan ta damu da kalubalen tsaro da ake fuskanta a hanyar Legas zuwa Ibadan, yana mai cewa, duk da haka, ta himmatu wajen tsara hanyar da za ta magance kalubalen tsaro da dabarun kawar da barazanar da ke tattare da babban hanyar.
Kazalika Ya yi kira ga masu amfani da hanyar, mafarauta, shugabannin al’umma, da sauran masu bin hanyar da su rika kai rahoton masu aikata laifukan ga yan sanda da sauran jami’an tsaro domin magance Matsalar cikin gaggawa.
A WANI LABARIN KUMA: Wani Gwamna A Kenya Ya Kori Ma’aikatan Bogi Masu Tarin Yawa
Gwamnan lardin Garissa na Kenya ya ba da umarnin cire sunayen Ma’aikatan bogi guda 3,000 da ke cikin jerin sunayen ma’aikatan lardin
An gano sunayen ne biyo bayan wani bincike da aka gudanar a kan ma’aikatan, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito