Wani fasto da ke Jihar Akwa Ibom, Ab Isong ta sanar da matarsa, Emem Isong cewa ta dena wahalar da kan ta saka rigar bacci da dare, LIB ta ruwaito.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce bata lokacinta take yi saboda dole ne a cire ta cikin dare.
KU KARANTA: Hoton fasto yayin da yake bankwana da mambobin cocinsa kafin ya wuce Aljanna, a cewarsa
Ya cigaba da cewa zuwa safe ba za ta ganta a jikinta ba, face a kasa yayin da komai ya kammala wakana tsakaninsu.
Duk da dai akwai wadanda ke ganin wannan maganar ta fi dacewa da su yi ta tsakaninsu a matsayinsu na ma’aurata.
Amma watakil akwai dalilin da ya sanya yake ganin dacewar ya yi mata ita a kafar sada zumuntar zamanin.
Ta yiwu ya yi ne don nishadi, ta yiwu kuma ya sanar da ita ne don ta dauki maganar a matsayin abu mai muhimmanci.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa:
“Ya ke Emem Isong, saka rigar bacci da dare bata lokaci ne saboda zuwa safe za ki tsince ta a kasa.”
Yayin mayar masa da martani, matar ta ce:
“Na lullube kaina da kariyar Jesus. Ba zan sake yi ba Ete.”
An kama faston da ke garkuwa da kansa a kai-a kai da zarar ya ji aljihunsa babu nauyi
Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato sun kama wani Albarka Sukuya, fasto bisa zarginsa da yin garkuwa da kansa, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana, ya tattara kudin fansa ne daga hannun mabiyarnsa bayan yin garkuwa da kansa.
Kafin a kama shi, an samu bayani kan yadda ya amshi N400,000 da kuma N200,000 a hannun mambobin nasa.
Dama ba wannan bane karonsa na farko ba. Kamar yadda jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Alfred Alabo ya bayyana, an kama wanda ake zargin ne a watan Nuwamban 2022.