Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa watau EFCC, reshen Jahar Borno ta gurfanar da Tijjani Haruna da Abdullahi Ahmed a gaban mai Shari’a Aisha Kumaliya, dake babbar Kotun Maiduguri, inda ta yanke musu hukuncin zaman gidan kurkuku na tsawon watanni shida bisa laifin yima hukumar EFCC karya. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Masu laifin dai sun karya dokar kundin kotun panel na sashi 139 na Jahar Borno.
Kamar yadda bayanin hukuncin yake ” Kai Tijjani Haruna, a wani lokacin a cikin watan Satumba na shekarar 2018 a Maiduguri Jahar Borno, karkashin kulawar wannan Kotu mai alfarma, ka baiwa hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa bayanin karya a shagonka na POS, a yayinda hukumar ke gudanar da bincike, wanda kasan bayanin karaya ne, wannan ya sabawa kundin kotun panel a sashi na 139, wanda hukuncin hakan na karkashin sashi na 139 na Kotun Panel dake Borno.”
KARANTA:-Gina kasa: Buhari ya baiwa jahohi biyar biliyan 143 don gyaran manyan tituna
Haka shima na biyun, yadda bayanin hukuncin yake ” Kai Abdullahi Ahmed, a wani lokacin a cikin watan Nuwamba na shekarar 2019 a Maiduguri Jahar Borno, karkashin kulawar wannan Kotu mai alfarma, ka baiwa hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa bayanin karya a shagonka na POS, a yayinda hukumar ke gudanar da bincike, wanda kasan bayanin karaya ne, wannan ya sabawa kundin kotun panel a sashi na 139, wanda hukuncin hakan na karkashin sashi na 139 na Kotun Panel dake Borno.”
KARANTA:- Likitoci masu neman kwarewa a Nigeria za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani
An dai same su da laifin da hukumar ke tuhumarsu dashi.
Mukhtar Ali Ahmed, Lauyan hukumar ta EFCC bayan kammala duba bayanan hujjojin da aka gabatar, ya bukaci kotu data gaggauta yanke musu hukunci.
Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke musu hukuncin zaman gidan kurkuku har na tsawon watanni shida tare da tarar kudade naira dubu ashirin kowannen su.