• “Sakamakon Gwajin Lafiyar Muhuyi na bogi ne”~ wani Masani a fannin kiwon lafiya.
• Wani ma’aikacin babban Asibitin kasa dake garin Abuja ya ce, ba zai yiwu ace asibiti ta bada irin wannan sakamakon ba, ma dauke da tarin kura-kurai.
• Sai dai wani babban jami’in asibitin ya ce, abashi cikakken lokaci kafin ya fitar da sakamakon karshe.
Haryanzu dai a na cigaba da nuna rashin tabbas, kan sakamakon Gwajin lafiya da dakataccen Shugaban hukumar karban korafe-korafen al’uma, da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin Gano, ya mika wa kwamitin wucin gadi na majalissar dokokin jihar, da aka kafa, domin binciken shi.
Magaji ya mika sakamakon Gwajin ne, domin ya zame mai sheda a kan rashin halartar shi taron da kwamitin ya shirya, domin Amma wasu tambayoyi.
Jaridar SAHELLIAN TIME ta ruwai to cewa, sakamakon ya janyo wasu tambayoyi da suke bukatar amsa.
Wani Masanin fannin kiwon lafiya dake aiki a Babban Asibitin kasa dake garin Abuja, Wanda kuma ya bukaci a sakaye sunan shi, ya yi watse da sakamakon da Muhuyi Magaji ya gabatar inda ya bayyana shi a matsayin “Na bogi”
KARANTA WANNAN LABARIN: Kan kammala tantance jaruman fim din Birnin Dala
Koda jaridar SAHELLIAN TIMES ta cigaba da tambayan Likitan, ya ce, Asibitin ba ta da bayanan wani mai suna “Muhuyi Magaji” Inji Masanin.
Ya kuma bayyana rashin gamsuwar shi, dangane da, saka hannun wani likitan asibitin mai suna Dakta Bayo, da aka gani a sakamakon gwajin lafiyan da aka gabatar wa majalissar dokokin jihar Kano.
Wani ma’aikacin asibitin shi ma ya bayyana cewa, babu yadda za’ayi ace, sakamakon gwajin lafiya daga asibiti ya fito da tarin kurakurai na rashin kwarewa haka, Kuma asibitin ta mika shi a hakan.
Ya ce” Muna aiki ne batare da amfani da takadda ba, Kuma dukkannin bayanan asibitin mu, Muna amfani da yanar gido ne, don haka, sakamako da rubutun hannu ba’a bukatar shi, kuma ba abu ne da zai yuwu ba” inji shi.
“Muna da wani tsare, wanda dole ne sai sakamako ya bi ta kanshi, kafin fitowar shi, wanda kuma wannan sakamakon bai bi ta kan wannan tsarin ba” kamar yadda ya bayyana.
Kazalika jaridar SAHELLIAN TIMES ta tuntubi wani baban jami’in asibitin, domin tabbatar da wannan batu, amma ya ce, a bashi cikakken lokaci kafin ya bayyana sakamakon karshe.
Amma duk yunkurin da a kayi, domin ji ta bakin Magaji abun ya citira, inda wayoyin shi suke a kashe.