Hukumar Jarabawar sharar fagen shiga Jami’a wato JAMB ta karyata rade radin dake yawo musamman a sabbin kafafen sada zumunta kan cewa sun sami matsala game da fitar da sakamakon daluban da suka zauna Jarabawara bana.
JAMB, ta karyata rade radin inda ta bukaci a dena yada jita jita a tsakanin Al’umma.
Babban kakakin hukumar Dakta Fabian Benjamin, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da yayi da manema labaru a Jihar Legas game da batun da yake yawo.
Dakta Fabian, yace babu wata matsala da suka samu game da sakin samakon daluban da suka Sami damar zana Jarabawar a bana.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar Daga hutun karshen makon daya gabata zuwa yau wata wasika ta zagaya duniya dauke da sakon cewar sakamakon Jarabawar dalubai ya sami matsala, hasalima ko wane dalubi zai kuma komawa inda ya rubuta Jarabawa don sake wata.
Sai dai JAMB din ta karyata batun, tace babu wata magana data danganci haka daga gare su, kawai dai suna kan tantance wasu daga cikin matsalolin da suka samu na sace-sace amsa (Malpractice) ko kuma makamacin haka, amma zasu Saki sakamakon nan da kwanaki kadan.
A wata tattaunawa da wakilin mu Shuaibu Abdullahi,yayi da wani matashi Wanda bai sami damar zana Jarabawar a bana ba saboda Naurar Kwamfuta ta kasa Tattance hannayen sa, yace hukumar JAMB din tace wai zata tafi da su Abuja chan babbar shelkwatar su inda zasu rubuta tasu jarabawar a chan.