A yammacin jiya Talata an Fafata wasannin rana ta 4 a gasar ajin Firimiya ta ƙasa da ake fafatawa mai taken Prudent Energy wasannin da ake fafatasu a babban birnin tarayya Abuja.
A jiyan dai an fafata wasannin ɓangaren maza kuma zakarar gasar wato Kano Pillars har yanzu nasara yakeyi a wasanni guda 4 data fafata bayan data kuma yin nasara a yau.
Ga jerin wasanni guda biyu da aka fafata da kuma sakamakon wasannin:
D defenders-28 – 23 Niger United.
2.Kano pillars 30 – 22 Borne Spiders.
A gobe za a shiga wasannin rana ta biyar tsakanin ƙungiyoyon ƙwallon hannu da dama a ɓangaren mata dana maza.
Sai dai da alamun bana gasar kowa zai iya lashewa biyo bayan yadda kowacce ƙungiya take taka rawar gani sosai da sosai.