Babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur Muhammad Sanusi Barkindo ya rasu, kuma ya bar duniya yana da shekaru 63.
Barkindo ya rasu ne a daren jiya, da misalin karfe 11 na daren Talata, kamar yadda Mele Kyari ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Kyari wanda shine shugaban kamfanin man Najeriya NNPC, ya sanar da rasuwar Barkindo ne da asubahin Larabar nan.
Ya bayyana rashin sa a matsayin babban rashi ga NNPC, OPEC, dama duniya baki daya, sakamakon irin ayyukan ci gaban da ya samar kuma yake kan samarwa.
Duk da cewa kawo yanzu ba a bayyana dalilin mutuwar tasa ba.
Lamarin ya kasance mai cike da ban al’ajabi, sakamakon yadda a jiya Talata, shugaban kasa Muhammad Buhari ya karbi Bakuncinsa a fadarsa dake Villa, tare da yaba masa dangane da irin gudunmawar da Barkindo ya bayar a kungiyar OPEC, tsawon shekaru 6 daya dauka yana shugabancin.