Sakatariyar Gwamnatin Tarayya ta kama da wuta a halin yanzu a Abuja
Wani yanki na Sakatariyar Gwamnatin dake a yankin Three Arms Zone a Abuja, a halin yanzu tana cin wuta.
Haka zalika, har yanzu ba’a san dalilin daya kawo gobarar ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Buhari ya gana da Jonathan a Abuja
Wasu daga cikin ababen hawa da lamarin ya shafa a halin yanzu yana cin wuta.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, jami’an kashe gobara sun isa wurin domin shawo kan gobarar.
A wani Labarin kuma
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yammacin yau Laraba, ya yi wata ganawar Gaggawa da Tsohon shugaban kasa Dakta Goodluck Jonathan, a fadar da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Tsohon Shugaban ya shiga harabar gidan Gwamnatin Nigerian ne da misalin karfe 4 na yammacin yau.
Sai har kawo hada wannan rahoto majiyar Jaridar Dimokuradiyya ba ta san dalilin da ya sa Jonathan ya ziyarci Shugaban kasa Buhari ba, saboda bai yi magana da manema labarai ba bayan bayan taron
Idan za’a iya tunawa, Jonathan ya kasance mai aiki a matsayin wakilin ECOWAS na musamman a kasar Mali, matsayin da ake tunanin cewa, shi ne ya kara kawo masa kusanci da Shugaba Buhari a ‘yan kwanakin nan.